Hebrews 10

Hadayar Kiristi Sau Ɗaya Tak

1Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa-wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za ta taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara shekara ba. 2Da a ce za ta iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtace masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. 3Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, 4domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yǎ kawar da zunubai ba.

5Saboda haka, saʼad da Kiristi ya shigo duniya, ya ce:

“Hadaya da sadaka kam ba ka so,
sai dai ka tanadar mini jiki;
6hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.
7Sai na ce, ‘Ga ni nan-a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi
na zo in aikata nufinka, Ya Allah.’ ”
Zab 40.6-8 (dubi Seftuwajin)

8Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). 9Saʼan nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yǎ kafa na biyun. 10Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

11Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba. 12Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah. 13Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa, 14gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.

15Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce:

16“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su
bayan wannan lokaci,
in ji Ubangiji.
Zan sa dokokina a cikin zukatansu,
in kuma rubuta su a kan zukatansu.”
Irm 31.33

17Sai ya ƙara da cewa:

“Zunubansu da kurakuransu
ba zan ƙara tunawa da su ba. ”
Irm 31.34

18In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya. 19Saboda haka, ʼyanʼuwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, 20ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, 21da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, 22bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. 24Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna-tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.

26Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za ta cinye abokan gāban Allah. 28Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama.”
M Sh 32.35
da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”
M Sh 32.36; Zab 135.14
31Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.

32Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, saʼad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.

35Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace. 36Kuna bukata ku jimre don saʼad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37Gama a cikin ɗan lokaci kaɗan,

“Mai zuwan nan zai zo ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38Amma mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.
In kuwa ya ja da baya,
ba zan ji daɗinsa ba.”
Hab 2.3, 4

39Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.

Copyright information for HauSRK